29 Maris 2026 - 22:22
Source: ABNA24
Iran Ta Kai Hari Kan Birnin masana'antu Na Neut Hawaf A Beer Saba'i

IRGC: A mayar da martani ga mummunan hare-haren da Amurka ta kai a kan cibiyoyin masana'antu na Iran, an kai hari kan birnin masana'antu na Neut Hawaf a cikin Beer Saba'a inda bayan harin garin ya turnike da hayaki tare da shiga cikin duhu da yankewar wuta gaba ɗaya 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ofishin Hulɗar Jama'a na Jami'an Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci: Bayan kai harin guguwar makamakai kashi na 86, a jerin hare-haren yaƙin Wa'adi Sadigh 4 bisa anbaton ramzin: "Ya Ilahal Alamiin" sadaukarwa ga duk 'yan wasa da zakarun kasa masu kishi, a matsayin martani ga mummunan hare-haren da Amurka ta kai kan masana'antu. Cibiyoyin Iran na Tekun Farisa, an kai hari kan birnin masana'antu na Neut Hawaf da ke Beer Assaba'a da ke kudu da yankunan da aka mamaye, an kai hari da makamai masu linzami na IRGC, kuma bayan fashewar wasu abubuwa da dama, yankin ya shiga wani yanayi na duhu gaba ɗayansa. Har ila yau, aikin ya kai hari kan sansanonin sojin Isra'ila da ke cikin hamadar Naqb, da Cibiyar rundunar yankin arewa, da cibiyoyin gwamnatin tsaro a birnin Kudus da aka mamaye, da Tel Aviv dukan su da makamai masu linzami na Iran tare da jiragen sama marasa matuka. 

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha